top of page

 

 

 Duk lokacin da wuta ta tashi a wani guri a doron qasa, sai ka ga Rahamar

Allah ta kawo xauki a gurin, wato ba ta zura ido tana gani a sakamakon makirci

da hassadar azzalumai, jikuna da gidajen waxanda ba su ji ba kuma ba su gani

 Wani Sufi yana hakaito qissar wani tsuntsu xan kwana-kwana, inda yake

cewa: tsuntsun domin kashe babbar wutar da azzalumai suka shirya wa Annabi

Ibrahim (AS), sai ya riqa xauko xigo-xigo na ruwa a bakinsa yana zuwa saman

harshen wutar nan yana xiga wa.

 Sai aka ce dashi:

 Waxannan xige-xigen ruwa ta yaya za su iya kashe wannan babbar wuta

 Sai tsuntsun ya ba su amsa kamar haka:

Na sani cewa ba za su iya kashewa ba, amma a lokacin da zalumaci ya faxo

akan masoyin Allah (Khalil-ul-lah), sai mutane suka kasu gida biyu, vangare

xaya masu laifi wato masu qetare iyaka da kuma xayan vangaren sune Adilai

kuma 'yan amana wato masu cika alqawari.

 To nima da wannan aikin ne nake son nuna tabbatuwa ta tare da vangaren

da yake akan daidai da kuma nuna barranta (nisanta) ta daga waxanda suka

kunna wutar, haka kuma ga waxanda suka yarda da aikinsu kuma suka qarfafa

 Addinin musulunci a mahangar Shi'a Imamiyya, kodayaushe ta hanyar

hikima da zaburar wa daga maganganu da ayyukan Tsarkaka (Alaihim-al-
salam) yake kira, kuma ta hanyar tabbatu wa akan alqawari da cika umarninsa

yake kira ga fito-na-fito da zalumci da munanan xabi'u da kuma hankulan ko

tunane-tunanen da suka kauce wa hanyar gaskiya.

 Kamar yadda alqur'ani mai tsarki ya tabbatar, yin wa'azi ko nasiha mai

kyau, biyayya da tsarkake wa, ya zama wajibi a kiyaye waxannan sharuda

 

1. Dole ne niyyar mutum tun daga fara aiki har zuwa qare shi, ta kasance

tsarkakakka kuma domin Allah Maxaukakin Sarki.

2. Dole ne tunane-tunane da fikirori su kasance a bisa ginshiqai

bayyanannu, daidai kuma nagartattu.

3. Haka kuma dole ne abubuwa da hanyoyin da za a yi amfani da su wajen

aiwatar da wannan al'amari, su kasance a samar da su ta hanyar da ta dace

kuma a yi amfani da su ta hanyar da ta dace, haka zalika dole hadafin

abun da za ayi ya zamo tsarkakakke kuma domin Allah ta yadda zai

kyakkyawar isa ga zuciya da hankalin xan adam.

Xan kwana-kwanan Tsuntsu

(tsuntsun da ya kawo xaukin kashe wuta)

bottom of page